Ma'aikatan Imo za su koma gona

Gwamna Rochas Okorocha Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manufar hakan, ita ce bunkasa ayyukan noma a jihar.

A Najeriya, gwamnatin jihar Imo ta mayar da kwanakin aiki zuwa uku, wato Litinin zuwa Laraba, maimakon biyar da aka saba.

Sauran kwanakin Alhamis da Juma'a kuma an mayar da su ranakun zuwa aikin gona.

Gwamantin ta ce ta bullo da sabon shirin ne domin ta karfafa wa ma'aikatanta gwiwar rungumar sana'ar noma gadan-gadan.

Sai dai ma'aikatan jihar sun bayyana fargaba game da wannan shiri.

Amma gwamnatin ta ce za ta bai wa ma'aikatan tallafin kudi mai sassaucin kudin ruwa.

Labarai masu alaka