Nigeria: Jihar Imo ta rage ranakun aiki

Gwamna Rochas Okorocha Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manufar hakan, ita ce bunkasa ayyukan noma a jihar.

Matsalar tattalin arziƙin da ta addabi Najeriya ta tilasta wa gwamnatin jihar Imo ta kudu maso gabashin ƙasar rage sa'o'in aiki ga ma'aikatan gwamnati.

A cewar gwamnatin, a yanzu ma'aikatan za su riƙa aikin kwana uku ne daga Litinin zuwa Laraba, sannan su tafi gona a ranakun Alhamis da Juma'a.

Gwamnan jihar, Rochas Okorocha, ya ce manufarsa ita ce ƙarfafa gwiwar ma'aikatan gwamnati su rungumi harkar noma, wacce aka daɗe da watsi da ita.

Gwamnatin ta ce za ta samar wa ma'aikatanta filayen noma, da iri, da duk wani taimakon da suke buƙata.

Sai dai ma'aikatan na fargabar cewa wannan wata dabara ce ta rage masu albashi—amma gwamnatin ta musanta hakan.

Labarai masu alaka