Indiya: Mutum 14 aka kashe a harin Assam

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aƙalla mutum 14 ne ake tunanin sun mutu a harin

Ƴan sanda a arewa maso gabashin Indiya sun ce wasu mayaƙan sa-kai da ake zargin ƴan wata ƙabila ne sun ce mutane akalla 14, sannan suka ji wa wasu fiye da 20 rauni yayin a wani hari da suka kai da bindigogi da kuma gurneti a kan wata kasuwa da ta cika maƙil.

Waɗanda suka shaida faruwar lamarin—a wani yanki na jihar Assam mai fama da tashe-tashen hankula—sun ce ƴan bindigar sun sanya kakin soji.

Ƴan bindigar dai sun kwashe minti 20 suna ɓarin wuta, lamarin da ya sa yankin ya yi kacakaca shaguna kuma suka ƙone.

Hukumomi sun ɗora alhakin faruwar lamarin a kan wata haramtacciyar ƙungiya mai yaƙin neman ƙwarya-ƙwaryar ƴancin cin gashin-kai ga ƴan ƙabilar Bodo.

Tun bara dakarun tsaro ke fafutukar murƙushe su.

Labarai masu alaka

Karin bayani