"An fitar da mu a jirgi don mun ambaci sunan Allah"

Hakkin mallakar hoto Nazia Ali
Image caption Iyalan sun je Paris shakatawa ne don murnar cikar su shekaru 10 da yin aure

An fitar da wani musulmi tare da matarsa daga jirgin sama bayan da wani ma'aikacin jirgin ya yi zargin cewa ya ga suna ta zufa suna ambatar sunan Allah.

Faisal Ali tare da matarsa Nazia Ali sun kwashe tsawon mintuna 45 suna zaune a cikin jirgin sama na Delta Air Lines lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa Cincinnati, a jihar Ohio ta Amurka kafin daga bisani wani ma'aikacin jirgin ya umurce su da su sauko za a yi musu tambayoyi.

Nazia Ali ta shaida wa manema labaru cewa " da muka nemi jin ko ana bukatar mu kwashe kayayyakinmu ne daga cikin jirgin sai ma'aikacin jirgin ya ce kwarai kuwa, saboda ba zaku dawo cikin jirgin ba".

Bayan an sauke su daga jirgin sun ga wani jami'an 'yan sanda a bakin kofa yana jiran su.

"Ta ce na firgita kwarai da naga wani mutum yana daukar hotunan Faspo din mu da wayar salularsa"

Bayan an yi musu tambayoyi kan dalilin zuwan su Paris, dan sandan ya ce bai da wata tambaya da zai kara yi wa iyalan wadanda suka je birnin domin shakatawa don murnar cikarsu shekaru 10 a matsayin mata da miji.

Daga bisani sun ce wani ma'aikacin jirgin ya shaida musu cewa matukin jirgin ne ya bukaci a sauke su, saboda daya daga cikin ma'aikatan jirgin ya ce hankalinsa bai kwanta ba saboda ya ce yaga Mr Ali yana boye wayar salularsa lokacin da yazo wucewa, kuma yana ta zufa yana ambatar kalmar "Allah".

Shi dai Mr Ali ya ce yana turawa mahaifiyar sako ne da wayar salularsa don shaida mata cewa suna cikin jirgi lafiya kuma ta shirya tarbarsu a filin jirgin sama na Cincinnati.

Ya kara da cewa mai yiwuwa rashin wadataccen iska a cikin jirgin ne yasa ya yi ta zufa saboda sun shafe kusan mintuna 45 suna zaune a cikin jirgin.

Kamfanin jirgin dai ya ba wadannan iyalai wadanda keda ‘ya’ya uku masauki inda suka kwana daya, yayin da wasu ma’aikatan hukumar hana fasakauri suka kara yi musu tambayoyi kafin daga bisani aka sa su cikin jirgin saman kamfanin don komawa gida.

Majalisar Musulmai ta Amurka dai ta rubuta takardar koke a kan kamfanin jirgin inda tace an nuna wa iyalan wariya.

Lauyan Majalisar, Sana Hassan ya ce “ Zargi a kan yadda suke mu’amala a matsayin wata barazana alama ce ta nuna wa Mr Ali da matarsa wariya kasancewar sun yi shiga irin ta musulmai”.

Sai dai kakakin kamfanin jirgin sama na Delta Air Lines Morgan Durrant ya ce kamfanin ya yi alla-wadai da duk wani nau’in nuna bambaci ga abokan huldarsa ba tare da la’akari da shekarunsu ko addini ko kuma jinsin su ba.

Ya kara da cewa kamfanin ya dukufa wajen mutunta dukkan abokan huldarsa, kuma kamfani zai gudanar da bincike tare da biyan daukacin kudin tikiti ga wadanda lamarin ya shafa”.