Nigeria ta doke Japan a gasar Olympic

Tambarin gasar Olympics Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A yau juma'a ne za a bude gasar wasanni ta Olympics.

Tawagar kwallon kafar Najeriya bangaren maza ta samu nasara a kan takwararta ta kasar Japan a gasar wasannin motsa-jiki na Olympics a birnin Rio.

Tawagar 'yan wasan Najeriya, Dream Team, ta doke Japan da ci 5-4 a gasar Olympic duk da cewa ba su isa birnin Rio na kasar Brazil da wuri ba, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin ya saba wa ka'ida.

A jiya da daddare ne aka yi wasan gabannin bikin bude gasar a hukumance.

Idan an jima ne za a gagarumin bikin bude gasar a hukumance.

Rahotanni daga birnin Rio da sauran biranen da za a yi wasannin gasar na cewa na dauki tsauraran matakan tsaro.

Mahkunta a kasar na fuskantar kalubale daga masu adawa da gasar, wandanda tun jiya Alhamis suka yi zanga-zanga, har wasu daga cikinsu suka yi yunkurin kashe fitilar gasar da ruwa a bokatai.

Labarai masu alaka