Yau za a bude gasar Olympics a Rio

Olympics
Image caption Yau za a bude gasar a hukumace.

Shugaban riko na kasar Brazil Michel Temer, ya ce ya na da kwarin gwiwar 'yan kasar za su yi farin ciki idan aka fara gasar wasannin Olympic a yau juma'a.

Mista Temer yace karbar bakuncin gasar da Brzil ta yi, duk kuwa da matsin tattalin arziki, da rikicin siyasa da kasar ke ciki ya nuna cewa za ta iya shawo kan matsalolin ta.

Kwamitin wasannin Olymics na kasar Rasha, ya an gama tantance 'yan wasa 271 daga cikin 387 da za su halarci wasan, yin da wasu biyar ke jiran a yanke hukunci na karshe.

Shugaban kwamitin Alexander Zhukov, yace Rasha za ta samu 'yan wasan da suka fi kowanne a gasar ta bana.

Tun da fari jagoran kwamitin gasar Olympics Thomas Batc, ya sanar da cewa a wannan karon masu shan kwayoyi ba za su taba sakata su wala ba, dan duk inda suke gwajin da za a gudanar a wurin zai fallasa su.

Labarai masu alaka