Rio 2016: An buɗe wasannin Olympic

Hakkin mallakar hoto Getty

Yayin buɗe wasannin Olympic karo na 31 a birnin Rio de Janeiro na Brazil, anyi bukukuwa a babban filin wasa na Maracana.

'Yan wasa daga kasashe fiye da 200 ne suka hallara domin fafata wasanni daban-daban.

Masu shirya wasannin sun yi alƙawarin tabbatar da wasannin sun ƙayatar ta hanyar nuna irin al'adun kasar Brazil da ta ƙunshi al'umma iri daban-daban.

Yanzu haka dai filin wasan cike yake maƙila da jama'a inda aka soma kade-kade da raye-raye.

Hakkin mallakar hoto AFP

Yayin bubukuwan bude wasannin ana ci gaba da amfani da hanyoyin nuna tarihin kasar ta Brazil.

An nuna yadda baƙar fata suka soma zuwa kasar a matsayin bayi dake cikin sarƙar bauta.

Ana kuma nuna irin tasirin al'adun Afirka a kasar ta Brazil.

Shahararren dan wasan ƙwallon ƙafa Pele bai samu damar kunna fitilar wasannin na Olympic ba.

Kunna fitilar dai aiki ne na girmamawa da a baya zakaran damben duniya marigayi Muhammad Ali ya yi.

Pele ɗan shekaru 75, yana fama da ciwon jijiyoyi, kuma an yi masa fiɗa a kwankwasonsa a farkon shekarar nan.

Hakkin mallakar hoto EPA

Sai dai kuma an kai ga shirya wasannin a Brazil ne cikin halin matsin tattalin arziki da kuma rikicin siyasa.

Dan haka ne ma aka tsaurara matakan tsaro, amma duk da haka masu zanga-zanga sun killace tituna a Copacabana.

Masu zanga-zangar suna nuna adawa da gwamnati, da kuma makuden kudaden da aka kashe wajen shirya wasannin na Olympic.

Wani ƙalubale kuma da aka fuskanta kafin a kai ga soma wasannin shi ne, fargaba dangane da cutar Zika.

Amma yanzu hankali zai koma ne ga yadda za a fafata gasa a wasanni 28, tsakanin ƙasashe 207 yayin wasannin na Olympic karo na 31

Labarai masu alaka