ANC ta sha da ƙyar a Afirka ta Kudu

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto
Image caption Badaƙalar cin-hancin da ta dabaibaye Shugaba Jacob Zuma ta rage wa ANC farin jini

Bayan ƙidaya kashi 92 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓukan ƙananan hukumomi a Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC mai mulki ta fuskanci koma-baya mafi muni tun kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

Sakamakon zaɓukan na ranar Laraba ya nuna cewa zuwa yanzu ANC ta sha kaye a hannun babbar abokiyar adawarta, Democratic Alliance (DA), a kwaryar birnin Nelson Mandela Bay mai matuƙar muhimmanci.

Jam'iyyun biyu dai na kankankan a yunƙurin lashe biranen Johannesburg da Pretoria.

Wani mai sharhi a kan al'amuran siyasar Afirka ta Kudu, Ranjeni Munusamy, ya ce kayen da ANC ta sha a Nelson Mandela Bay—wanda aka raɗawa sunan gwarzon ƙwatar ƴanci na ANC ɗin kuma shugaban kasar na farko Nelson Mandela—mummunar illa ce da jam'iyyar ba za ta taɓa warkewa ba.

Sai dai jam'iyyar ta ANC ce ke kan gaba a faɗin ƙasar, da kashi 54 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.

Tun bayan da aka kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata fiye da shekara 20 da ta gabata dai ANC kan lashe sama da kashi 60 cikin ɗari na ƙuri'un da ake kaɗawa.

Rashin aiki da badaƙalar cin-hanci da rashawa da ta shafi Shugaba Jacob Zuma sun shafa wa ANC baƙin fenti.

Sharhi: Tasirin ANC na raguwa, Milton Nkosi, Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban jam'iyyar DA Mmusi Maimane ya ce jam'iyyarsa ta bai wa mutane zabi

A iya cewa waɗannan zaɓuka ne saƙo mafi girma da masu kaɗa ƙuri'a suka aike wa jam'iyyar ANC tun bayan kafuwar dimokuraɗiyya a Afirka ta Kudu a 1994.

A zahiri har yanzu ANC na da gagarumin goyon baya a faɗin ƙasar, amma goyon bayan na raguwa. A yanzu ta bayyana ga jam'iyyar cewa lokacin naɗe hannu saboda tabbacin da take da shi cewa baƙar fatar ƙasar masu rinjaye na binta sau-da-ƙafa ya wuce.

Ƙarfin faɗa-a-ji da tasirin da take da su na raguwa.

Rikicin cikin gida, da cecekuce a bainar jama'a, da badaƙalar cin-hanci da rashawa na zagwanye ƙimar da jam'iyyar ke da ita sannu a hankali.

Kyakkyawan misalin haka shi ne abin da ya faru a Nelson Mandela Bay, wanda jam'iyyar DA ta lashe--yankin da ya ƙunshi Port Elizabeth mai tarihin gwagwarmayar ƙin jinin mulkin wariyar launin fata. Sabon magajin garin yankin dan jam'iyyar DA, Athol Trollip, farar fata ne.

Shekara 22 bayan kawo ƙarshen mulkin wariya baƙar fata sun fara yin zaɓe bisa la'akari da batutuwan da suka damu al'umma a maimakon launin fata.

Da al'ummar baƙar fata masu rinjaye ba su zaɓe shi ba, babu yadda za a yi Mista Trollip ya yi nasara, duk da cewa ya iya harshen Xhosa sosai.

Labarai masu alaka

Karin bayani