Afirka ta Kudu: Za mu koyi darasi —ANC

Mataimakin Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Image caption Mista Ramaphosa ya ce ANC jam'iyya ce mai sauraron talaka

Mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce jam'iyyar ANC mai mulki za ta koyi darasi daga koma-bayan da ta fuskanta a zaɓukan ƙananan hukumomin da aka gudanar.

Bayan samun sakamakon kashi 98 cikin ɗari na zaɓen dai, goyon bayan da ANC ke samu ya ragu matuƙa musamman a waɗansu biranen ƙasar masu muhimmanci.

Mista Ramaphosa ya ce, "Suna ganin mu masu girman kai ne, suna ganin mu masu ɗagawa ne, suna ganin mu masu son zuciya ne, amma zan so na musanta duka waɗannan tunane-tunanen; mu mutane ne masu sauraron jama'a".

Jam'iyyar ta ANC ta sha kaye a hannun babbar abokiyar adawarta, Democratic Alliance (DA), a Nelson Mandela Bay, birnin aka laƙabawa sunan jarumin gwagwarmaya da wariyar launin fata kuma tsohon shugaban ƙasar, Nelson Mandela.

Sai dai ga alama babu jam'iyyar da za ta samu rinjaye kwaf-ɗaya a biranen kasuwanci na Johannesburg da Tshwane, wanda ya haɗa da babban birnin ƙasar, Pretoria. Tuni aka fara tattaunawar haɗin gwiwa a yankunan.

Farouk Chothia, mai yi wa BBC sharhi a kan al'amuran Afirka ta Kudu, ya ce goyon bayan da ANC ke samu a birane ya tarwatse ne bayan da baƙar fata masu matsakaicin samu da ma'aikata suka koma bayan jam'iyyar DA.

Ya ƙara da cewa wannan wani lamari ne mai cike da tarihi da ke nuna ƙOsawar jama'a da almundahana da gazawar ANC ta cika alƙawuran da ta yi.

Sharhi: Tasirin ANC na raguwa, Milton Nkosi, Afirka ta Kudu
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban jam'iyyar DA Mmusi Maimane ya ce jam'iyyarsa ta bai wa mutane zabi

A iya cewa waɗannan zaɓuka ne saƙo mafi girma da masu kaɗa ƙuri'a suka aike wa jam'iyyar ANC tun bayan kafuwar dimokuraɗiyya a Afirka ta Kudu a 1994.

A zahiri har yanzu ANC na da gagarumin goyon baya a faɗin ƙasar, amma goyon bayan na raguwa. A yanzu ta bayyana ga jam'iyyar cewa lokacin naɗe hannu saboda tabbacin da take da shi cewa baƙar fatar ƙasar masu rinjaye na binta sau-da-ƙafa ya wuce.

Ƙarfin faɗa-a-ji da tasirin da take da su na raguwa.

Rikicin cikin gida, da cecekuce a bainar jama'a, da badaƙalar cin-hanci da rashawa na zagwanye ƙimar da jam'iyyar ke da ita sannu a hankali.

Kyakkyawan misalin haka shi ne abin da ya faru a Nelson Mandela Bay, wanda jam'iyyar DA ta lashe--yankin da ya ƙunshi Port Elizabeth mai tarihin gwagwarmayar ƙin jinin mulkin wariyar launin fata. Sabon magajin garin yankin dan jam'iyyar DA, Athol Trollip, farar fata ne.

Shekara 22 bayan kawo ƙarshen mulkin wariya baƙar fata sun fara yin zaɓe bisa la'akari da batutuwan da suka damu al'umma a maimakon launin fata.

Da al'ummar baƙar fata masu rinjaye ba su zaɓe shi ba, babu yadda za a yi Mista Trollip ya yi nasara, duk da cewa ya iya harshen Xhosa sosai.

Labarai masu alaka

Karin bayani