South Sudan: Za'a tura dakarun wanzar da zaman lafiya

Hakkin mallakar hoto

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta amince a tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar wadanda zasu shawo kan yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tangal-tangal.

A baya dai gwamnatin ta yi watsi da wannan shawara, sai dai kuma daga bisani ta amince saboda matsin lambar da ta fuskanta a wajen wani taron gaggawa da akayi a Addis Ababa babba birnin kasar Habasha.

Sai dai kuma gwamnatin Sudan ta Kudun da kuma shugabannin kasashen yankin sun ce har yanzu ba a amince akan yawan dakarun da za a tura ba da kuma ranar da za a turasun ba .

Rikicin baya bayan na tsakanin dakarun da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma na babban abokin adawarsa Riek Machar sun yi barazanar sake dawo da yakin basasar da akayi a shekarar 2013.