'Yan tawaye sun afka sansanin soji a Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hadakar kungiyar 'yan tawaye a Syria ta ce mayakansu sun afkawa wani sansanin soji mafi girma da ke arewacin birnin Aleppo.

Sansanin dai shi ne wajen da yan tawayen ke hari domin su tarwatsa shirin da gwamnatin ta yi na yi musu kofar rago a gabashin Aleppo inda fararen hula dubu dari biyu da hamsin suka makale.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for human rights ta tabbatar da cewa an kama wani bangare a sansanin.

Wani hoton bidiyo da 'yan tawayen suka saki ya nuna 'yan tawayen a cikin sansanin inda suke duba irin makamai da kayan aikin da aka kwace.

Labarai masu alaka