Kungiyar I-S ta hallaka direbobin tasi 5 a Iraqi

Hakkin mallakar hoto

Jami'an tsaro a Iraqi sun ce mayakan I-S sun hallaka wasu direbobin tasi biyar da suka zarga da ficewa da fararen hula daga yankunan dake karkashin su.

An tilastawa mazauna yankin da suka hada da iyalan direbobin, kallon yadda ake aiwatar da kisan a kan su a yammacin birnin Qaim.

Mayakan sun yi gargadin cewa duk wanda ya yi wani yunkuri na tserewa daga yankin zai fuskanci irin wannan hukunci.

Kungiyar ta I-S ta jima tana yin barazana ga fararen hular dake yankunan da suke rike da iko, tare da tilasata musu cigaba da zama a inda suke.