Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 12 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto EPA

Akalla mutane goma sha biyu ne suka mutu a birni mafi girma a Pakistan, Karachi sakamakon ambaliyar ruwa ta kwanaki biyu.

Fiye da rabin mutanen da suka mutun, wutar lantarki ce ta kashe su, yayin da sauran kuma, gini ya fada musu.

Sabon shugaban lardin Sindh, inda birnin Karachi yake, ya kai ziyara wuraren da ambaliyar ta shafa.

Ya ce jami'ai na kokarin yashe ruwan da ke kan hanyoyi, da gyara wutar lantarki da ta yanke.

Ya kuma bukaci al'ummomin Karachi da su yi aiki tare don bunkasa kyawun muhallin birnin.