'Yan Najeriya ba su gamsu da matakan tsaro ba

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu 'yan Najeriya sun ce ba su gamsu da salon da jami'an tsaron kasar ke dauka na yaki da masu sace-sacen jama'a don neman kudin fansa da fashi da makami ba.

'Yan Najeriyar na nuna damuwa ne yayin da jami'an tsaro ke cewa suna ci gaba da fama da fafutikar yaki da masu tafka irin wannan laifuka ba.

Masu nuna rashin amincewar dai na ganin bai kamata jami'an tsaro su rika shelar matakan da suke shirin dauka ba, maimakon hakan, kamata ya yi su karade dukkan wani lungu da sako da ake zargi 'yan ta'adda na boyewa don fatattakar su.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai 'yan sandan Najeriya suka yi shelar fara yaki da masu sace-sacen jama'a don neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja a wani biki da suka gudanar a garin Katari.

Labarai masu alaka