Sarkin Japan Akihito zai sauka daga mulki

Hakkin mallakar hoto

Sarkin Japan Akihito ya bayyana ra'ayinsa na sauka daga mulkin.

A wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar, sarkin ya bayyana damuwarsa kan yadda shekru da kuma yanayin lafiyarsa nan gaba kadan za su hana shi gudanar da ayyukansa yadda yakamata.

Dan kimanin shekaru tamanin da biyu da haihuwa, sarki Akihito ya ce yana fatan al'ummar Japan za su fahimci yanayin da yake ciki.

Ana kyautata zaton nan gaba kadan firaministan kasar Shinzo Abe zai fitar da sanarwa.

An nada sarki Akihito akan matsayinsa ne shekaru 27 da suka gabata bayan mahaifinsa Hirohito ya mutu.