Za a binciki shugaban 'yan wasan Kenya

Image caption Kenya ta fuskanci cikas wajen shiga gasar Olympics saboda karya ka'idojin amfani da abubuwan kara kuzari

Hukumar yaki da abubuwan kara kuzari tsakanin 'yan wasa ta kasar Kenya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin cin hanci akan shugaban tawagar 'yan wasan tseren kasar.

Jaridar Sunday Times ta Burtaniya ta fitar da wani hoton bidiyo da aka dauka a asirce da ya nuna Manjo Michael Rotich na tayin yi wa 'yan wasa gargadi na zuwan jami'an da ke gwajin abubuwan kara kuzari inda aka ba shi cin hanci.

Sai dai rahotanni sun ce Manjo Rotich ya musanta aikata ba daidai ba, inda ya ce ya je tare da 'yan jaridar da suka yi shigar burtu ne domin yana son ya san ko su wanene.

Kasar Kenya dai ta fuskanci cikas wajen shiga gasar wasannin Olympics saboda zarge-zargen karya ka'idojin amfani da abubuwan kara kuzari tsakanin 'yan wasa inda sai a ranar Juma'a ne aka bayyana wa kasar karara cewa za ta shiga gasar.

Labarai masu alaka