Farashin kayan abinci 'ya sauko' a Nigeria

Masu sayar da kayan abinci a Najeriya sun ce girbin da aka fara yi ya sa kayan na abinci dangin hatsi ya sauko.

Matakin dai wani abin karfafa gwiwa ne ganin yadda farashin ya yi matukar hauhawa a kwanakin baya, lamarin da ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Wakilinmu Mukhtari Adamu Bawa ya je wata babbar kasuwa a birnin Kano da ke arewacin kasar, ya kuma tattauna da wani mai sayar kayan abinci:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka