Za a fara jigilar alhazan Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maniyyata fiye da dubu hamsin ne za suje aikin hajjin bana daga Najeriya

A Najeriya, a ranar Litinin ne ake sa ran fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana zuwa kasar Saudi-Arabiya, inda za a kaddamar da aikin a birnin Sokoto da alhazan jihar Zamfara.

Kimanin maniyyata hajjin kusan dubu hamsin da takwas ne daga jihohi za su je kasa mai tsarki, sai kuma alhazai dubu takwas da dari biyar daga kamfanoni masu zaman kansu.

Ta waya Aisha Shariff Baffa ta tuntubi shugaban hukumar alhazai ta Najeriya, Abdullahi Mukhtar Muhd inda ta soma da tambayarsa ko kamfanoni nawa ne za suyi jigilar alhazan?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka