Pistorius ya musanta yunkurin kashe kansa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pistorius na zaman gidan fursuna ne bayan da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru shida

Tsohon dan wasan Olympics dan kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius ya musanta cewa ya yi yunkurin hallaka kansa a gidan yari.

A ranar Asabar ne aka garzaya da dan wasan asibiti inda aka yi masa magani sakamakon raunin da ya ji a wuyan hannunsa.

Jami'ai a gidan yari sun ce raunin da dan wasan ya ji bai da girma sosai, kuma tuni aka mayar dashi gidan fursuna.

A cewar jami'an, dan wasan ya shaida musu cewa ya fado ne daga kan gadonsa.

Sai dai wata Jarida a kasar mai suna City Press ta ce wani mutum da ke tsare a gidan fursunan ya shaida mata cewa da gangan dan wasan ya ji wa kansa rauni.

Jaridar ta kara da cewa an gano reza a dakin da Pistorius ke zaune a gidan yarin bayan da aka gudanar da bincike.

A watan da ya gabata ne masu shigar da kara suka ce daurin shekara shida a gidan kaso da aka yanke wa dan wasan ya yi sauki sosai inda suka ce za su daukaka kara.

Labarai masu alaka