An rantsar da Idriss Deby a karo na biyar

Hakkin mallakar hoto Buhari Office

A Ndjamena, babban birnin kasar Chadi, an yi bukukuwan rantsar da Shugaba Idris Deby, domin yin wa'adin mulki na biyar.

Gabannin fara bikin rantsuwar, 'yan hamayya sun yi ta zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da Mista Deby ya ci gaba da mulki, lamarin da ya haddasa mutuwar akalla mutum guda.

Shugabannin kasasashe da dama sun halarci bikin, ciki har da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Mulkin Deby

Janar Idriss Deby mai ritaya ya karbi mulkin kasar Chadi ne a shekarar 1990 bayan ya jagoranci tawayen da ya kawo karshen mulkin Shugaba Hissene Habre.

An yi zaben raba-gardama wanda ya kawo sauyi ga tsarin mulkin kasar, wanda ya bai wa Shugaba Deby damar tsaya wa takara ya kuma yi nasara a watan Yunin 1996.

Shugaba Deby ya kara lashe zabe a shekarar 2001.

Kuma kasar ta tsunduma cikin yakin basasa tsakanin Musulmi da Kirista a shekarar 2005, yayin da aka yi yunkurin yi masa juyin mulki ta hanyar harbo jirginsa a shekarar 2006, amma hakan bai yi nasara ba.

An yi zaben raba-gardama a watan Yunin 2005 wanda ya soke dokar wa'adi biyu ga shugaban kasar, kuma ya bai wa Deby damar sake tsayawa takara.

A ranar 8 ga watan Agusta ne kuma aka kara rantsar da Deby a matsayin shugaban kasar a shekarar 2006.

An sake rantsar da shi a wa'adi na hudu a watan Afrilun shekarar 2011, bayan ya samu gagarumin rinjaye a babban zaben kasar.

Kuma a farkon wannan shekarar aka sake yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul tare da maido da tsarin wa'adi biyu ga shugaban kasa.

Yayin da kuma ya yi ratsuwar ci gaba da mulki a karo na biyar a ranar 8 ga watan Agustan 2016.

Tarayyar Afrika

Shugaba Idriss Deby shi ne yanzu shugaban kungiyar Tarayyar Afrika bayan ya karbi mukamin daga shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, a watan Janairun 2016.

A yanzu dai Shugaba Deby yana auren Hinda wadda ta haifa masa 'ya'ya biyu Mahamat da Brahim.

Ko da yake ya auri wasu matan kafin ita, yana kuma da wasu 'ya'yan.