Dumamar yanayi ta rage yawan Kifin da ake kamawa a Duniya

Wani sabon bincike da akayi ya gano cewa, karuwar dumamar yanayin da ake samu a karnin da ya gabata, shi ne babban dalilin da ya sa aka samu koma baya a yankunan da akafi kamun Kifi.

Tafkin Tanganyika da ke gabashin Afrika, wuri ne da ke da muhimmanci ga miliyoyin mutane wajen samun abinci, amma kuma a 'yan shekarun baya-bayan nan an samu raguwa a yawan Kifayen da ake kamawa.

Da ana ganin yawan kamun Kifin ne dalili, amma kuma masana kimiyya sun gano cewa matsalar dumamar yanayi ta dade ta na illa ga tafkin.

Sun ce, saboda yawan zafin da ake yi a yankin ya sa sinadaran da ke kasan tekun ba sa iya tasowa saboda zafi.