Dagaci ya yi wa yarinya fyaɗe a Jigawa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rundunar Hisbah na cikin hukumomin da suka tashi tsaye domin yaki da masu fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa da ke Najeriya ta ce ta kama wani dagaci bisa zargin yi wa wata karamar yarinya fyade.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdu Jinjiri, ya shaida wa BBC cewa sau da dama dagacin na garin Kargo a karamar hukumar Garki, Abubakar Ya'u, yana hilatar yarinyar a kan hanyarta ta zuwa makaranta, inda yake yi mata fyade sannan ya ba ta kudi.

A cewarsa, an gurfanar da dagacin a gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.

Abdu Jinjiri ya kara da cewa rundunar 'yan sandan ta kuma kama mutum 32 bisa zargin yi wa kananan yara mata fyade, yayin da aka kama mutum 25 bisa zargin aikata luwadi daga watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Ya yi kira ga mutane da su rika sanya idanu sosai a kan 'ya'yansu, yana mai bukatarsu da su mika wa rundunar rahoton duk wani wanda ya yi wa 'ya'yan nasu fyade.

Labarai masu alaka