'Yan bindiga sun kashe sojoji a Naija Delta

Image caption An tura sojoji ne domin hana fasa bututan mai

Wasu 'yan bindiga a garin Nembe da ke jihar Bayelsa ta Najeriya sun kashe sojoji uku a lokacin wani hari da suka kai musu a ranar Litinin.

Jama'in tsaro da mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun kuma kwashe makaman sojojin sannan suka tsere a cikin wani karamin jirgin ruwa.

Sun kara da cewa mai yiwuwa 'yan bindigar sun kwace akalla jiragen ruwa guda uku na sojojin, wadanda aka kai wa hari a lokacin suna bakin aiki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa 'yan bindigar sun yi shiga irin ta limaman coci ne.

Sojojin dai na cikin dakarun da aka tura yankin domin sanya ido kan bututan man fetur.

Wannan lamari dai na faruwa ne kwanaki kadan bayan wasu mutane sun kashe sojoji 11 lokacin da suka yi musu kwanton-bauna a jihar Naija da ke arewacin kasar.

Masu fafutika a yankin na Naija Delta dai sun matsa kai hare-hare, inda suke fasa bututan man fetur.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe masu tayar da kayar bayan.

Labarai masu alaka