An kai hari a wani asibitin Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firai Ministan Pakistani Nawaz Sharif ya bayyana matukar kaduwa

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani asibiti da ke Quetta a kasar Pakistan ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 63.

Jami'ai a kasar sun ce fiye da mutum 120 ne suka samu raunuka a harin, wanda aka kai a bangaren kula da masu larurar gaggawa na asibitin.

A daidai wurin ne aka kai gawar wani fitaccen lauya na kasar wanda aka harbe har lahira a safiyar ranar Litinin.

Mutanen da suka mutu sun hada da lauyoyi da 'yan jaridar da ke raka gawar lauyan mai suna Bilal Anwar Kasi.

An yi ta harbi da bindigogi bayan harin.

Ba a san kungiyar da ta kai harin ba har yanzu.

Wasu 'yan bidiga ne dai suka harbe Mr Kasi, wanda shi ne shugaban kungiyar lauyoyi ta Balochistan, a kan hanyarsa ta zuwa babbar kotun da ke Quetta.

Labarai masu alaka