An hallaka mutane 70 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'ai a Pakistan sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a kan wani asibiti da ke Quetta ya yi sanadin mutuwar mutane 70.

Yayin da wasu kusan 120 suka jikkata a harin wanda aka kai a kofar sashen bayar da kulawar gaggawa, inda gawar wani fitaccen lauyan da aka harbe a ranar Litinin ta ke.

Wadanda lamarin ya rutsa da su dai sun hada da lauyoyi da kuma 'yan jarida da suke raka gawar Bilal Anwar Kasi.

Wani bangare na kungiyar Taliban ya dauki alhakin kai harin.

Haka kuma kungiyar ta Jamaat-ul-Ahrar ta ce ita ce ta kashe lauyan, wanda shi ne shugaban kungiyar lauyoyi na kasar a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kotu.

Firai minista Nawaz Sharif da hafsan sojin kasa, janar Raheel Sharif duka sun ziyarci inda lamarin ya auku.

Labarai masu alaka