Nigeria: Za a sasanta rikicin PDP

Image caption PDP ta shiga rudani ne tun bayan zaben 2015

A Najeriya, kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta PDP ya kafa wani karamin kwamiti karkashin jagorancin tsohon ministan watsa labarai Farfesa Jerry Gana domin sasanta bangarorin da ke rikici da juna game da batun shugabancin jam'iyyar.

Jam'iyyar PDP ta fada cikin wani yanayi na rudani ne tun bayan data sha kaye a babban zaben kasar na shekarar 2015.

Yanzu haka dai jam'iyyar ta rabu gida biyu tsakanin bangaren Senata Ali Madu Shariff da kuma bangaren Senata Ahmed Makarfi inda kowannen su ke ikirarin kasancewa halastaccen shugaban jam'iyyar.

Senata Walid Jibrin, shi ne shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar, ya kuma yiwa Yusuf Tijjani karin bayani kan matakan da suke dauka don dinki barakar data janyo rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan Jam'iyyar, ga yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka