BH: Sojoji na neman Salkida ruwa-a-jallo

Ahmad Salkida
Image caption Ahmad Salkida ya musanta cewa yana da alaka da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana neman dan jaridar nan, Ahmad Salkida, wanda ke da kusanci kungiyar Boko Haram ruwa-a-jallo kan sace 'yan matan Chibok.

Sojojin na kuma neman Ambassada Ahmed U. Bolori da kuma Aisha Wakil, wadanda ta ce suna dauke da wasu bayanai masu muhimmanci amma sun ki bai wa hukumomi.

Kakakin rundunar sojin Kasar, Kanar Sani Usman Kuka Sheka, ya shaida wa BBC cewa mutanen uku na da alaka da kungiyar ta Boko Haram.

Ahmad Salkida, yana da kusanci da Boko Haram, kuma shi ne ke wallafa yawancin bayanansu a mafi yawan lokuta.

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ahmad Salkida na amfani da shafukan sada zmunta sosai

Kungiyar na tura masa faifan bidiyo da hotuna kai tsaye, amma sai dai ya ce su da kansu suke wallafa bidiyonsu a yanar gizo.

Salkida yana zaman gudun hijira ne yanzu a Dubai, bayan ya bar Najeriya saboda a cewarsa ana yi wa rayuwarsa barazana.

A lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi kokarin shiga tsakanin gwamnati da Boko Haram domin ceto 'yan matan Chibok, amma yunkurin bai yi tasiri ba.

A wata hira da ya yi da BBC a bara, Salkida, ya musanta cewa yana da alaka da kungiyar, yana mai cewa aikinsa kawai yake yi na jarida.

Labarai masu alaka