Shugaban Sao Tome da Principe ya ji 'tsoron' shiga zabe

A wani mataki na ba safai ba, shugaban kasar Sao Tome and Principe ya kauracewa zaben shugaban kasar zagaye na biyu, lamarin da zai bai wa babban abokin hamayyarsa nasara.

Manuel Pinto da Costa ya janye daga shiga zaben ne, wanda aka gudanar ranar Lahadi, yana zargin cewa an tafka magudi a zagayen farko na zaben da aka yi ranar 17 ga watan Yuli.

Yanzu dai babban abokin hamayyarsa, Evaristo Carvalho, wanda tsohon Firai Ministan kasar ne, yana da tabbacin lashe zaben.

Ya samu kashi 49.8 cikin dari , yayin da Mr Pinto da Costa ya samu kashi 24.8 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Mr Pinto da Costa ya gallazawa 'yan kasar ta Sao Tome a shekara 15 da ya kwashe yana mulkin kasar, wacce ta samu 'yancin kanta daga Portugal a shekarar 1975.