Danbarwa tsakanin Trump da jiga-jigan jam'iyyarsa

Hakkin mallakar hoto Getty

Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin dan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Republican Donald Trump da kuma wasu manyan jami'ai da suka yi aiki a karkashin gwamnatin shugaba Bush a kan harkar tsaro.

Jami'an dai sun fitar da wata sanarwa inda suka soki Mr Trump da cewa ba shi da kwarewa da kuma kimar da ake bukata ta zama shugaban kasa.

Sun yi hasashen cewa idan har ya samu nasara, zai kasance shugaban Amurka wanda ya fi kowanne shashanci da rashin tsari a tarihi.

Da yake mayar da martani, Mr Trump ya ce su wadannan mutane na daga cikin manyan shugabannin siyasa na Amurka wadanda za a dorawa alhakin jefa duniya ta zama cikin hadari.