Ana cin zarafin 'yan cirani a Austarlia

Sansanin 'yan cirani na Nauru Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Ana cin zarafin yaran ta hanyar llata da su.

An wallafa wasu bayanai, kan karuwar cin zarafin yara da ake yi a sansanin da ake tsare da 'yan cirani a tsuburin Nauru da ke Australia.

Jaridar The Guardian ta Birtaniya, ta wallafa irin abubuwan da ta gani a cikin wasu takardu sama da dubu biyu, da suka bayyana hoton abinda ke faruwa da ya hada da cin zarafin yara ta hanyar yin lalata da su, da musguna musu, da kokarin hallaka kai da matasa da ke neman mafaka ke yi saboda tsananin azaba.

The Guardian ta wallafa cewa akwai wata yarinya da ta ke cikin mawuyacin halin da ta kai ta dinke labbanta, da kuma wani yaro da masu gadin sansanin ke yi wa barazanar hallakawa.

Sai dai gwamnatin Australia ta ce tuni aka fara gudanar da bincike kan zarge-zargen, alhakin tabbatar da hakan ya rataya ne a wuyan 'yan sandan Nauru.

Labarai masu alaka