Barazi- Dilma Rousseff na fuskantar tsigewa

Dilma Rousseff Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun a watan Mayu aka dakatar da ita daga shugabancin Brazil.

Fiye da kashi biyu cikin uku na 'yan Majalisar Dattijan Brazil ne suka kada kuri'ar amincewa da gurfanar da tsohuwar shugabar kasar Dilma Rousseff a gaban shari'a.

Ana dai zargin Mis rousseff da laifin kashe kudin gwamnatin ba bisa ka'ida ba, ba kuma tare da amincewar 'yan majalisa ba, da daukar bashi a bankunan kasar da nufin cike gibin kasafin kudin Brazil na shekarar 2014.

An dai dakatar da ita daga mukamin ta ne a watan Mayun shekarar, duk da cewa ya musanta zarge-zargen da ake ma ta.

Idan har aka sauke ta daga mukamin shugabar kasa, shugaban rikon kwarya Michel Temer na zai ci gaba da jagorantar kasar har zuwa lokacin da za a yi zabe a shekarar 2018.

Labarai masu alaka