Masana sun yi batur mai narkewa

Hakkin mallakar hoto ASHLEY CHRISTOPHERSON

Batur din dai siriri ne, kuma yakan narke da zarar an saka shi a rana, ko wuri mai zafi, ko kuma idan aka saka shi cikin ruwa ko danshi.

Batur din yana da karfin bolti 2.5, sannan yana da karfin cajin raskwanar jikin kwamfuta.

Za a iya amfani da batur din wajen adana bayanan sirri irin na soji; haka kuma zai taimaka wajen sa ido a kan al'amuran da suka shafi muhalli.

Furofesan aikin injiniya a jami'ar jihar Iowa, Reza Montazami ya ce wannan ne karon farko da aka kirkiro batur mai narkewa a zahiri.

An dai gano cewa ba za a iya amfani da batur din a jikin Dan'adam ba, saboda yana dauke da sinadarin lithium, amma a halin da ake ciki masana na bincike a kan yanda batur din zai narke a jika ba tare da ya cutar ba domin a huta da radadin da ake sha wajen cire shi na tsawon shekaru

Labarai masu alaka