'Matan Masar ne na ɗaya wajen dukan miji'

Matan Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matan dai kan fakaici ido su sanyawa mazan kwayar sanya bacci, kana su lakada musu duka.

Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta nuna cewa matan kasar Masar su ne na daya a duk duniya wajen duka da cin mutuncin mazajensu.

Bayan Masar sai kuma Burtaniya, yayin da kasar Indiya ke matsayi na uku a wannan dabi'a.

Kamar yadda alkaluma daga kotun sauraren kararrakin da suka danganci iyalai ta Masar ta rawaito, kashi 66 cikin 100 na matan auren da suke cin zarafi da dukan mazajensu, suna neman kotun ta raba auren.

Rahoton ya nuna cewa, su kuwa mazajen da suka dandana kudarsu a hannun matayen nasu, ba su da wata hanya ta samun kariya daga irin wannan ukuba sai dai kawai su gurfanar da matan nasu gaban kotu, inda a yanzu ake da irin wadannan kararraki 6,000 a kasar.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna matan na yin amfani da makami ko belet, ko ,muciya, ko tabarya da sauran su wajen dukan mazajen.

Wasu matan sai sun bai wa mazajen kwayoyin da za su sanya su barci a boye domin su samu damar dukansu ko ma su kona su.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka