Matar da ta yi shekara 16 'bata ci abinci ba'

Hakkin mallakar hoto IAN THOMAS JANSEN LONNQUIST

Fitacciyar mai fafutikar nan 'yar kasar India, Irom Sharmila, ta shaida wa wata kotu cewa za ta kawo karshen yajin cin abincin da ta kwashe shekara 16 tana yi.

Sai dai a cikin wadannan shekaru, an tilasta mata cin abinci sau da dama a gadon asibitin da aka kwantar da ita.

An gan ta tana shiga kotun tare da rakiyar ma'aikatan jinya guda biyu, inda daga bisani ta shaida wa alkali cewa ta dakatar da yajin cin abincin.

Sharmila ta fara yajin cin abincin ne domin bijirewa wata doka mai karfin gaske da ta bai wa sojoji damar murkushe masu tayar da kayar baya a garinsu na Manipur.

Ta ce ta janye daga yajin cin abincin ne domin tsayawa takara a zaben da za a yi a yankin a matsayin 'yar takara mai zaman kanta.

Labarai masu alaka