Isra'ila ta tsare mata da jaririya a filin jirgi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An gurfanar da Galit a gaban kotu a ranar Talata bisa zargin jaririyar ba 'yarta bace

Hukumomi a Isra'ila na tsare da wata mata da jaririyarta a filin jirgin sama na Tel Aviv, bayan komawarsu kasar daga Sri Lanka a ranar Asabar.

Za a yi wa matar mai suna Galit Nakash gwajin kwayoyin halitta domin tabbatar da cewa ita ta haifi jaririyar.

Jami'an Isra'ilar sun ce idan gwajin ya tabbatar ba 'yarta ba ce to za a mai da ta Sri Lanka.

An hana matar shiga kasar ne bayan ma'aikatan filin jirgin sun gano cewa Galit ta yi amfani da wani fasfo da ba na 'yarta ba.

Matar ta ce ta haifi jaririyar, Tahel ne a lokacin da ta je aiki a Sri Lanka, kuma ta nemi ayi mata fasfo amma jami'an ofishin jakadancin suka ki.

Kuma sun nemi ta yi gwajin kwayoyin halitar a can amma ta ki saboda bata yarda da su ba.

A cewar lauyan matar mai shekaru 49, Matan Hodorov an mai da Galit da jaririyarta 'yar shekara daya kurkukun Ayalon har sai an samu sakamakon gwajin a ranar Juma'a mai zuwa.