EFCC ta saki mawallafi a shafin intanet

Hakkin mallakar hoto efcc
Image caption Ibrahim Magu, shugaban EFCC

Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta saki mawallafin shafin intanet din nan, Abubakar Saddiq Usman.

Wani makusancin mawallafin ya tabbatarwa da BBC sakin Abubakar.

A ranar Litinin ne dai EFCC ta kama Abubakar a gidansa da ke unguwar Kubwa bisa zargin laifin aika sakonnin barazana ta intanet, abin da hukumar ta ce ya sabawa doka.

Sai dai wasu rahotanni na cewa an kama shi ne saboda ya rubuta wani labari a kan shugaban hukumar, Ibrahim Magu, wanda bai yi wa EFCC dadi ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da na masu fafutika a shafukan intanet na Najeriya sun soki hukumar ta EFCC bisa tsare mawallafin.

Kungiyar SERAP da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma kare hakkin dan adam ta zargi EFCC da wuce gona da iri kan kamun Sidiq Usman.

Ita ma kungiyar matasa ta jamiyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi tur da kamun nasa, tana mai cewa yunkuri ne na yin kafar ungulu ga dokar fadin albakarcin baki.

Daman dai hukumar ta EFCC ce ta ba shi beli kuma za ta sake shi idan ya gabatar da mutanen da za su tsaya masa.

Labarai masu alaka