An daure wani kan kisan Musulmi a Scotland

An yanke wa wani mutum hukuncin shekaru 27 a kurkuku, bayan samunsa da laifin kisan wani mai shago a birnin Glasgow na Scotland.

Kotu ta samu Tanveer Ahmed mai shekaru 32 da laifin kisan Mr. Shah, wanda ya zarga da yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

An daba wa mista Shah wuka ne a yayin da ya ke shagonsa da ke Glasgow.

Mamacin dai wani fitaccen ɗan Ahmadiyya ne.