Trump ya kunna wutar sabuwar takaddama

Hakkin mallakar hoto AP

Dantakarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ya kunna wutar wata sabuwar gardama, kasancewar ya bukaci masu goyon bayan tsarin mallakar bindiga da su jajirce wajen ganin cewa abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat, wato Hillary Clinton ba ta tauye musu 'yancinsu ba.

Wasu dai na ganin kiran da Donald Trump ke yi cewar a dauki mataki a kan Hillary Clinton tamkar kokari ne na tunzura mutane domin su far ma abokiyar hamayyar tasa.

Ga alama Donald Trump ya yi wannan furucin ne a kokarin da yake yi na daidaita yakin neman zabensa, bayan wani jerin katobarar da yi ta yi a dan tsakanin nan.

A jawabin da ya yi ga wani taro a North Carolina, Mr Trump ya ce idan aka zabi Hillary Clinton a matsayin shugabar kasa, to za ta samu damar nada alkalai, wadanda za ta sarrafa su wajen yin gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin Amurka tare da soke ikon mallakar bindiga kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin kasar, yana cewa "idan ta samu sukunin nada alkalanta shi kenan taku ta kare."

Wasu dai na fassara wannan farucin da cewa zunzurutun zuga ne ko kuma ingiza mai kantu ruwa, ta yadda za a tunzura masu bindiga yin amfani da makaminsu a kan alkalai ko kuma Mrs Clinton.

Ofishin yakin neman zaben Clinton din dai ya yi tir da wadannan kalamai na Donald Trump, yana bayyana su da cewa suna da hadari. Kodayake, Kakakin Mr Trump din a nasa bangaren ya musanta cewa yana kokarin tunzura jama'a ne da kalaman nasa, domin su tada fitina.

Kakakin ya ce babu wani abu a cikin maganar face kokarin da Mr Trump ke yi na ankarar da masu kare 'yancin Amurkawa na mallakar bindiga domin su fita kwansu da kwarkawata wajen shure duk wani yunkuri na yin garambuwal ga kundin tsarin mulkin kasar.