Recep Erdogan na ziyara a Rasha

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A watan Yuni ne Rasha ta ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Turkiyya

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan, ya isa birnin St. Petersburg domin gyara dangantakarsa da Rasha.

Wannan ce ziyarar mista Erdogan ta farko tun bayan yunƙurin juyin mulkin da aka yi masa da bai yi nasara ba.

Kuma a yayin ziyarar shugaban na Turkiyya zai gana da shugaban Rasha, Vladimir Putin.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu ne a watan Nuwambar bara, bayan Turkiyya ta harbo jirgin yaƙin Rasha a kan iyakarta da Syria.

Lamarin da ya sa Rasha ta sanya wa Turkiyya takunkumin cinikayya tare da dakatar da shirin yawon bude idon da 'yan Rashan ke zuwa yi a Turkiyyan.

Shugaba Putin dai ya yi kalaman da ke nuna cewa yana son su daidaita da ƙasar ta Turkiyya.

Labarai masu alaka