Zika na ci gaba da yin barazana a Amurka

Jariri mai dauke da cutar Zika
Image caption Jami'an lafiya na shawartar matafiya su takaita zirga-zirga, dan gudun kamuwa da cutar.

Gwamnan jihar Florida a Amurka Rick Scott, ya yi kira ga 'yan majalisar dokokin kasar su gaggauta samar da kudaden da za a yaki kwayar cutar Zika, bayan samun karin mutane 4 da suka kamu da cutar a Miami.

Wannan dai shi ya kawo adadin mutane 21 da suka kamu da cutar ta Zika, kuma dukkan mutanen sun kamu da cutar ne a gundumar Wynwood.

A lokacin da ta kai ziyara Miami, 'yar takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrats Hillary Kiranta, ta sa ke kira ga 'yan majalisar kan batun samar da kudaden.

Ana danganta cutar Zika da haifar jarirai da dan karamin kai da tawaya a kwakwalwarsu.