Sojin Rasha su janye daga Aleppo na sa'o'i

Mayaka a birnin Aleppo
Image caption Yakin Syria dai ya daidaita miliyoyin al'umar kasar.

Sanarwar dakatar da bude wuta na sa'o'i uku a kowacce rana da sojin Rasha suka sanar ta fara aiki a birnin Aleppo.

Rasha ce dai ta ayyana dakatar da bude wutar domin bada dama kayan agaji su isa yankunan birnin da fararen hula suka makale saboda gwabza fadan da ake yi da dakarun gwamnati da na 'yan tawaye.

Jami'an lafiya a birnin sun ce akalla mutane 4 ne suka mutu wasu da dama suka jikkata a harin da ake kyautata zaton anyi amfani da iska mai guba da aka hada da sinadarin Chlorine.

Sai dai babu tabbas din ko su ma 'yan tawayen Syria za su dakatar da bude wuta ya yin kai kayan agajin ga fararen hula da ke tsananin bukatar taimako.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi koarfin cewa sa'o'i uku sun yi kadan a gudanar da wannan aiki.

Labarai masu alaka