An sace $750,000 a jirgin ƙasa a India

Hakkin mallakar hoto Express Photo
Image caption A ranar Talata ne dai aka yi satar

'Yan sanda a jihar Tamil Nadu a ƙasar Indiya sun fara bincike kan wata sata da aka yi ta dala 750,000 a cikin wani jirgin ƙasa.

Ɓarayin dai sun ɓalla rufin ƙarfe na taragon jirgin wanda ke ɗauke da daruruwan akwatunan da aka zuba takardun kuɗin da suka lalace.

Kuɗaɗen dai na babban bankin ƙasar ta Indiya ne.

'Yan sanda na bincike kan yadda aka yi satar duk da tsauraran matakan tsaron da ke jirgin ƙasan.

Sai bayan da jirgin ya isa inda za shi sannan aka gano cewa an yi satar.

Labarai masu alaka