Gobara ta kashe jarirai a Iraq

Ana samun karin rahotannin tashin gobara a kasar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana samun karin rahotannin tashin gobara a kasar

Akalla jarirai bakwaini 11 ne suka mutu a wani asibiti da ke Bagadaza na kasar Iraki sanadiyar tashin wata gobara.

Wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta ce gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Talata, a bangaren masu haihuwa na asibitin koyarwa na Yarmouk da ke yammacin birnin.

Sanarwar ta kara da cewa an samu ceto wasu jarirai bakwai da mata 29 kuma an maida su wasu asibitocin.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa an bai wa jarirai 19 magani na kunan da suka samu da kuma shakar hayakin da suka yi.

Ma'aikatar lafiyar ta ce watakila gobarar ta tashi ne sakamakon matasalar da aka samu ta wutar lantarki.

Babu cikakken bayani kan batun, sai dai ana samun rahotanni na karuwar gobara sanadiyar matsalar wutar lantarki a ma'aikatu da manyan kantuna a kasar a 'yan shekarun nan.