Amurka: An nemi haurawa gidan Trump

Donald Trump Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ginin dai anan ne Mista Trump da iyalan sa ke zaune.

'Yan sanda a birnin New York sun cafke wani mutumin da ya yi kokarin haura dogon ginin gidan Trump Tower da ke birnin.

Mutumin dai na kokarin dare katangar ginin da aka yi ta da gilashi mai hawa hamsin da takwas, inda ya shafe sa'o'i masu yawa yana wannan yunkuri.

Ginin dai mallakar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ne, kuma a nan hedikwatar yakin neman zabensa take, da kuma iyalansa.

A halin yanzu dai Mista Trump ba ya birnin New York din, ya tafi yakin neman zabe a cikin kwaryar Amurka.

Kawo yanzu ba a tabbatar da dalilin da ya sanya mutumin yin wannan yunkurin shiga gidan dantakarar ba.

Labarai masu alaka