BBC Hausa na neman ma'aikatan wucin-gadi

Image caption BBC ce kafar labaran da ta fi kowacce girma a duniya.

Sashen Hausa na BBC na neman'yan jaridar da suke da gogewar aiki a gidan rediyo da talabijin, ko wadanda suka naƙalci kafafen sadarwa na zamani domin hulɗa da su a zaurensa na aikin jarida.

Sashen zai ba su damar samun horo tare da bunƙasa su a fagen aikin rediyo da talabijin da sauran kafafen sadarwa na zamani.

Kuma wadanda suka samu nasara bayan kammala horon, za a dauke su aikin wucin-gadi a ofisoshinmu da ke birnin Abuja na Najeriya da Accra na Ghana.

Muna bukatar 'yan jaridar da suka samu gogewa a aikin jarida, musamman farautar labarai da yada su. Ana bukatar masu neman shiga shirin su kasance sun san jama'a sosai da muhimman kafafen samun labarai, da yadda za su yi amfani da sanayyar wajen hada labarai.

Kazalika wajibi ne mai son shiga shirin ya fahimci shirye-shiryenmu a kafofin sadarwa na zamani da kuma dandalin zumunta, tare da naƙaltar yanda basirarsa za ta taimaka wajen jan hankalin sabbin masu sauraro.

Haka kuma wajibi ne mai son shiga shirin ya kasance ya iya sararrafa harshen Ingilishi da daidaitacciyar Hausa da kuma ka'idojin rubutu.

Za a bukaci ka dinga zuwa wajen horarwa daga mazauninka da bai wuce tafiyar sa'a daya ba daga wadannan birane biyun, wato Abuja da Accra. Sannan ana son samun ka a duk lokacin da bukata ta taso a zangunan aikin da muke da su daban-daban a cikin mako. Kuma yana da muhimmanci ka kasance mai sha'awar aikin dare.

Masu sha'awar shiga shirin za su iya turo bayanin karatu da ayyukan da suka yi a baya da kuma jawabin da bai dara sakin layi guda ba a kan abin da ya ba su sha'awar shiga shirin ta wannan adireshin, wato: westafrica.recruitment@bbc.co.uk daga nan zuwa 31 ga watan Augusta 2016

Labarai masu alaka