Boko Haram: Za a sa ido kan masu wa'azi a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane da sunan addinin musulunci

A Najeriya, gwamnatin jihar Borno ta kafa wata hukumar malaman addinin musulunci da za su rika sanya ido kan ayyukan malamai masu wa'azi a yankunan kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Haka kuma an dora wa hukumar alhakin baza masu leken asiri zuwa garuruwa da kauyuka daban-daban, domin jin irin hudubar da malamai ke yi a masallatai na tsattsauran ra'ayi.

Manufar hakan inji gwamnan jihar, Kashim Shettima, wanda ya kaddamar da hukumar a birnin Maiduguri ita ce dakile yaduwar akidar tsattsauran ra'ayin addini da ya kai ga samuwar kungiyar Boko Haram.

Hukumar ta kunshi malamai daga manyan kungiyoyin addinin musulunci na kasa wato Izala da kuma darika, a karkashin jagorancin babban limamin jihar ta Borno, Imam Zannah Ibrahim Ahmed.

Labarai masu alaka