Musulmi mata na cikin kangi a Birtaniya

Image caption Musulmi mata na son taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban dan adam

Wani rahoto da majalisar dokokin Birtaniya ta fitar ya ce Musulmi mata na samun koma-baya a fannin tattalin arzikin kasar.

Rahoton ya gano cewa musulmi mata suna fuskantar yiwuwar rashin samun aiki sau uku idan aka kwatanta da sauran mata.

Ya bayyana wani mawuyacin hali da matan suka fi fama da shi - wato kasancewarsu mata da kasancewarsu daga tsirarun al'umma da kuma kasancewarsu Musulmi.

'Yan majalisar sun ce ya kamata ministoci su bullo da wasu tsare-tsare masu inganci da za su kawo karshen wannan matsala kafin karshen shekarar nan.

Wani mai magana da yawun gwamnatin kasar ya ce yanzu musulmi mata kashi 45 cikin 100 na yin aiki idan aka kwatanta da shekara biyar da suka wuce, ko da yake ya amince cewa akwai bukatar zage dantse domin taimaka musu.

Labarai masu alaka