Mata ma'aikata sun samu tagomashi a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kafin amincewa da dokar mata ma'aikata na hutun makonni 12 ne

Majalisar dattawan India ta amince da wani kudurin doka wanda zai ninka kudaden da ake biyan mata ma'aikata a lokacin hutun haihuwa.

Sabuwar dokar ta bai wa mata damar hutun haihuwa har na tsawon makonni 26.

Gwamnati na fata matakin zai karfafa gwiwar mata masu ilimi da suka ƙware a wasu fannoni su ci gaba da aiki bayan sun fara tara iyali saboda rabinsu kan ajiye aiki ne a halin yanzu.

Dokar za ta kuma amfani matan da suke rainon yaran da ba su suka haifa ba, da wadanda ke daukar ciki domin haifa wa wasu ya'ya.

Har ila yau dokar ta ce wajibi ne ma'aikatu da kamfanonin da ke da ma'aikatan da suka haura mutum 50, su samar da wurin kula da jarirai.

Indiya na daya daga cikin kasashen da ke da karancin mata ma'aikata a duniya - abin da gwamnati ke matukar son ganin ta sauya domin habaka tattalin arzikin kasar.

Labarai masu alaka