Za a fara riga-kafin cutar Polio a Nigeria

Ana yiwa jariri riga-kafin Polio Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Polio na saurin yaduwa, dan haka hukumomi a Najeriya suka sha alwashin daukar matakan gaggawa dan shawo kan lamarin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan da kwanaki 10 za a fara yin allurar riga-kafi cutar Polio, bayan sake barkewar cutar a arewacin Najeriya.

Yara biyu aka tabbatar da sun kamu da cutar a kananan hukumomin Jere da Gwoza a jihar Borno, shekaru biyu kenan da ba a samu wanda ya kamu da cutar ba.

Jagoran asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, mai kula da riga-kafin Polio Reza Hossaini, ya sanar da cewa za a fara yi wa yara miliyan biyar allurar riga-kafin cutar a jihohin Borno, da Yobe da kuma Adamawa masu makoftaka.

Ya kara da cewa bai yi mamaki ba da cutar ta sake bullowa, wannan dalili ne ma ya sanya Majalisar Dinkin Duniya ke jiran shekaru uku kafin ta ayyana kasa da wadda ta yi sallama da cutar.

Jihar Borno dai nan ne cibiyar Boko Haram, inda mutane sukai gufdun hijira sassa daban-daban na kasar da ma kasashe makofta.

Labarai masu alaka