Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Muna goyon bayan tantance malamai- Zakariyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin jihar Borno ta fito da shirin ne dan magance yaduwar tsattsauran ra'ayi tsakanin al'uma.

A Najeriya, gwamnatin jihar Borno ta kafa wata hukumar malaman addinin musulunci da za su rika sanya ido kan ayyukan malamai masu wa'azi a yankunan kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Haka kuma an dora wa hukumar alhakin baza masu leken asiri zuwa garuruwa da kauyuka daban-daban, domin jin irin hudubar da malamai ke yi a masallatai na tsattsauran ra'ayi.

A game da hakan Abdou Halilou ya ji ta bakin Ustaz Husseini Zakaria wani mai wa'azin a Abuja:

Labarai masu alaka